Kotun Ƙoli ta amince da buƙatar gwamnatin tarayya da ke ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na soke tuhume-tuhumen da ake yi wa Nnamdi Kanu, jagoran ƙungiyar IPOB mai neman ɓallewa daga Najeriya.
Kotun Ƙolin ta ce dole ne Kanu ya fuskanci shari’a.
A watan Oktoban bara ne, wata kotun ɗaukaka ƙara ta bayar da umarnin a saki Mista Kanu inda ta ce akwai kura-kurai a shari’ar.
Sai dai gwamnati ta sake shigar da ƙara inda ta ce Kanu barazana ne ga tsaron Najeriya.