Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce, yakin Ukraine ya faro ne daga kwace yankin Cremia, kuma zai kare ne da kwato shi daga hannun Rasha.
Mr Zelensky na jawabi ne ‘yan awanni bayan wasu hare-hare ta sama kan sansanonin sojin Rasha da ke can, da suka yi sanadin mutuwar mutum daya.
Ya ce, zaman dakarun Rasha masu mamaya a Cremia barazana ce ga Turai da ma zaman lafiya a fadin duniya, don haka raba ta da shi, shi ne a’ala.
Shekaru takwas kenan da Rasha ta kwace yankin Cremia na Ukraine wanda ya faru a 2014. In ji BBC.