Hare-haren da aka kai wa Rasha “ba za su wuce ba tare da martani ba”, a cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha.
Maria Zakharova ta faɗa wa ‘yan jarida cewa Ukraine ce ta kai harin, kuma ta ce harin da ake kaiwa cikin Rashar ba zai yiwu ba ba tare da bayanai daga ƙasashen Yamma ba.
Wasu daga cikin jirage marasa matuƙa da suka hari birnin Moscow cikin dare sun faɗa kan wani filin jirgi a Pskov mai nisan kilomita 600 daga Ukraine.
Ya zuwa yanzu, Ukraine ba ta ce komai ba – da ma ba su fiya cewa komai ba game da hare-haren da ake kaiwa cikin Rasha. In ji BBC.


