Manyan mutane daga yankin Inyamurai karkashin inuwar Igbo Elders Consultative Forum, sun yi wani taro na Kungiyar IECF, wadda ta bayyana muradin da ta ke da shi a zaben shugaban kasa mai zuwa da za ayi a 2023.
Chukwuemeka Ezeife ya yi jawabi, ya na gargadi Ibo a kan neman kujerar mataimakin shugaban kasa.
Jaridar Vanguard rawaito cewa, kungiyar Igbo Elders Consultative Forum ta yi zama a ranar Laraba, 16 ga watan Fubrairu 2022, inda suka yanke shawara a kan takarar 2023.
Kungiyar ta ce, dole ne shugaban kasa na gaba da za a yi, ya fito daga yankinsu na Kudu maso Gabas.