fidelitybank

Dole ne sai an biya ‘yan Fansho kafin a biya ma’aikatan gwamnati – Otti

Date:

Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya bayar da umarnin cewa dole ne ma’aikatan gwamnati da masu karbar fansho a jihar Abia su karbi albashinsu kafin a biya masu rike da mukaman siyasa albashi.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ya koka kan yadda gwamnatocin da suka gabata a jihar suka dade suna bin ‘yan fansho, kafin daga bisani gwamnatinsa ta wanke kudaden fansho da ba a biya ba.

Gwamna Otti ya bayyana haka ne a sakonsa na Easter ga ‘yan asalin jihar Abia, yana mamakin dalilin da ya sa aka hana ma’aikatan gwamnati da suka yi wa jihar hidima na tsawon lokaci mai tsawo.

Ya yi nuni da cewar bai kamata biyan mutane kudaden fansho ya zama abin burgewa ba amma ya bayyana cewa farin cikin da ke cikin fuskokin wadanda suka yi ritaya ya samo asali ne daga basussukan da ake bin su na tsawon lokaci.

“Hakika abin takaici ne a ce wadannan manya maza da mata (’yan fansho), wadanda suka yi wa kasa aiki a kololuwar shekarun da suka yi na samun ci gaba, an dade ana bin su.

“Ko ta yaya, kamar yadda na ambata a cikin jawabina ga Abians jim kadan bayan rantsar da ni, ba za a sake fuskantar manyan ‘yan kasarmu da azabar rashin biyansu hakkokinsu ba.

“Tun daga nan na ba da umarnin a biya cikakken kudaden fansho ko kafin ranar 28 ga wata, a ranar ne ma’aikatan gwamnati ke samun albashin su.

“A bisa ka’ida, masu rike da mukaman siyasa za a biya su ne kawai bayan an cika nauyin da ya rataya a wuyanmu ga manya da ma’aikatan gwamnati, gaba daya,” in ji Gwamna Otti.

Ya godewa shuwagabannin kungiyar da ‘yan kungiyar ’yan fansho ta Najeriya a jihar kan yadda suka amince da gwamnatinsa, inda ya jaddada cewa jin dadin al’ummar Abia na da matukar muhimmanci ga gwamnatinsa.

Ya bayyana cewa Abia ta zama daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a kasar nan kuma ya shawarci ‘yan asalin Abia da masu ziyara da su zagaya da saka hannun jari a jihar ba tare da tsoro ba.

Ya taya al’ummar Abia da Kirista baki daya murnar bikin Ista na bana, yana mai cewa babu wani yanki na jihar da za a bar shi ba tare da ci gaban sa ba.

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp