Shugaban ƙasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya shaida wa shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin cewa dole a ƙawo ƙarshen rikicin Ukraine.
Kalaman nasa na zuwa ne lokacin da suka ziyarci Putin a ranar Asabar a garin St Petersburg da ke Rasha, wanda hakan wani ɓangare ne na yunkurin shiga tsakani domin samar da zaman lafiya kan rikicin Ukraine da Rasha.
A ranar Juma’a ne Shugaban Ukraine ya shaida wa tawagar cewa shi ba zai yi wata tattaunawa da Rsha ba har sai dakarunta sun fice daga iyakar ƙasarsa.
Tawagar dai ta tafi da ƙunshin shawarwari da take ganin idan dai an bisu za su iya sake gina zaman lafiyar ƙasashen biyu.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce, cikin shawarwarin akwai ficewar dakarun Rasha daga Ukraine da kuma janye ƙudurin kama Shugaba Putin da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta ɗauki niyya.


