Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya yabawa shugaba Bola Tinubu na Najeriya bisa “karfin jagoranci. ”
Biden ya yi tsokaci na musamman kan yadda Tinubu ya yi maganin rikicin da juyin mulkin Jamhuriyar Nijar ya haddasa.
Shugaban na Amurka ya kuma amince da matakan da gwamnati mai ci ta dauka na “gyara tattalin arzikin Najeriya”.
Daga nan sai Biden ya gode wa Tinubu kan “karfin shugabancinsa” a matsayinsa na shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, wajen kare dimokuradiyya da kiyaye doka a Nijar da ma sauran yankuna.
Biden ya kara da cewa, “Gayyatar Najeriya zuwa taron G20, amincewa da muhimmiyar rawar da Najeriya ke takawa a duniya a matsayin dimokiradiyya da tattalin arziki mafi girma a Afirka yayin da sojoji suka kwace,” in ji Biden.


