Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ce kungiyar da yake jagorantar Jama’atu Nasril Islam, za ta nemi a tabbatar da adalci ga mutanen da harin jirgin sojojin Najeriya maras matuki ya aukawa bisa kuskure a cikin jihar Kaduna.
Sarkin Musulmi ya ba da wannan tabbaci ne yayin babban taron kungiyar Jama’atu Nasril Islam na shekara-shekara a ranar Litinin din nan, daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sake neman afuwa a kan abin da ya faru, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
“A matsayinmu na cikakkun Musulmai, mun dauka cewa abin da ya faru kaddara ce daga Allah kuma za mu duba, mu ga abin da za mu iya yi ga wadanda wannan harin ya shafa, za mu tabbatar da mun yi ta bibiya don ganin an yi adalci.
“Ba ma ganin kowa amma muna son ganin an yi wa kowa adalci. A matsayinmu na Musulmai dukkanmu mun ji takaici kan abin da ya faru,” a cewarsa.
Game da taron na Jama’atu Nasril Islam, Sarkin Musulmi ya ce an tsara shi ne don tattaunawa kan batutuwan da ke faruwa a fadin duniya game da Musulmai da kuma addinin Musulunci.
Ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta mayar da hankali wajen gyaran titunan kasar musamman titin Minna zuwa Suleja da Minna zuwa Bida wadanda ke cikin mummunan yanayi a jihar Neja.
A jawabinsa, ministan yada labarai na Najeriya, Alhaji Mohammed Idris ya sake nanata neman afuwar Shugaba Bola Tinubu da kuma jajantawa kan mummunan harin jirgin sama maras matuki da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane da jikkata wasu da dama a garin Tudun Biri.
Ya ce shugaban kasar ya amince da fara shirin FULAKO, wanda zai ba da damar gina gidaje da kananan asibitoci da makarantu da dakunan kula da lafiyar dabbobi a wani bangare na bin matakan da ba na soji ba, ga rikice-rikicen ‘yan fashin daji da na satar mutane don kudin fansa a arewa.