Hukumar ƙwallon ƙafa ta Saliyo, ta ƙaddamar da bincike bayan an ci ƙwallaye ɗari da tamanin da bakwai a gasar wasan kwalon kafar kasar a wasanni biyun farko da aka buga.
Hukumar ƙwallon ta ce, za ta bincki jami’ai da ƴan wasa kan yadda aka yi har ƙungiyar Gulf FC ta ɗura wa Koquima Lebanon ƙwallaye 91 da 1 yayin da kuma Kahula Rangers ta yi wa Lumbenbu United ruwan ƙwallaye har 95 ba ko daya.
Idan har aka tabbatar da sahihancin kwallaye da aka zura, wasan zai kasance wanda aka fi zura kwallaye a cikinsa a tarihin ƙwallon ƙafa a duniya. In ji BBC.