Kocin Manchester United, Erik ten Hag, ya ce “a bayyane yake” dalilin da ya sa ya yanke shawarar siyan dan wasan gaba a bana, bayan da kungiyarsa ta sha kashi da ci 2-0 a Tottenham Hotspur ranar Asabar.
An danganta kungiyar da ‘yan wasan gaba da suka hada da tsohon tauraron Spurs, Harry Kane, wanda ya koma Bayern Munich a makon jiya.
Amma Ten Hag ya kulla yarjejeniya da Rasmus Højlund mai shekaru 20 a yarjejeniyar da ta kashe fan miliyan 64 da wani karin fam miliyan 8.
Bayan ganin kungiyarsa ta kasa cin kwallo a filin wasa na Tottenham, Ten Hag ya amince zuwan Højlund, wanda har yanzu bai fara buga wasa ba saboda rauni, ya dace.
“Mun yi imanin wadannan ‘yan wasan, a bara ma, za su iya zura kwallaye. Hakanan a bayyane yake dalilin da yasa muka sanya hannu kan dan wasan gaba.
“Idan komai ya yi kyau, Martial na kan hanyar dawowa, Højlund ma yana zuwa, don haka za mu sami karin ‘yan wasa da za su zira kwallo a raga. ‘Yan wasan da ke filin wasa kuma za su iya zura kwallaye,” in ji Ten Hag.