Tsagin tsohuwar jam’iyyar All Nigeria Peoples Party wato ANPP da ke cikin babbar jam’iyyar APC da ke mulki a Najeriya sun ce lallai ne a bar musu kujerar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027, inda suka buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi watsi da buƙatar nemo wani daban.
Tsagin ANPP ɗin sun ce su ne na biyu wajen ƙarfi a haɗakar da aka yi a shekarar 2013 da ta haifar da jam’iyyar APC, inda suka yi barazanar cewa yin watsi da su a tikitin takarar zaɓen 2027 zai iya tilasta musu su fara tunanin sauya sheka daga APC, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ƙungiyar tsofaffin mambobin ANPP ne suka bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, inda suka ce ba a saka musu yadda ya dace ba bisa babbar gudunmuwar da suka bayar wajen kafa jam’iyyar APC.
Jagoran ƙungiyar Farfesa Vitalis Orikeze Ajumbe ya ce, “za a samu matsala a takarar 2027 idan aka ɗauki wanda ba ɗan tsagin ANPP ba a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.”
Ya ce tsaginsu na ANPP ya sha wahala tare da fuskantar wariya a zamanin mulkin Marigayi Muhammadu Buhari.
Ya ce daga cikin mambobin su akwai mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da gwamnoni irin su Babagana Umara Zulum na jihar Borno da Mai Mala Buni na jihar Borno da tsofaffin gwamnoni irin su Attahiru Bafarawa da Sani Yarima Bakura da Ali Modu Sheriff da sauran su.