fidelitybank

Dole ne a yaba wa Tinubu – Maryam Shetty

Date:

Matar nan da shugaba Bola Tinubu ya cire sunanta daga cikin jerin sunayen da ya aike wa majalisar datawa don tantance su a matsayin ministocin gwamnatinsa Dakta Maryam Shetty ta ce, ƙaddara ce ta sa a ka cire sunanta.

Cikin wani dogon saƙo da ta wallafa a shafiunta na Facebook Maryam Shetty ta ce ba za ta iya bayyana irin farin cikin da ta ji ba a lokacin da ta ga sunanta cikin jerin mutanen da ake son nadawa a matsayin ministocin kasar.

Kuma hakan a cewarta wata alama ce da ke nuna cewa a shirye Najeriya take wajen tabbatar da kyakkyawar makomar mata musamman matasa a kamarta.

To sai dai Dakta shetty ta ce ƙaddara wadda ta riga fata ta yi tasiri wajen cire sunanta daga jerin sunayen.

Ta ce ”wasu na ganin hakan tamkar wani koma-baya ne a gareni, amma ni a matsayina na musulma na yadda da ƙaddara, na ɗauki hakan a matsayin ƙaddara daga Allah, wanda shi ke bayar da mulki ga wanda ya so, kuma a lokacin da ya so”.

Ta kuma ƙara da cewa duk, da wannan abin da ya faru, tana miƙa godiyarta ga shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu kan sanya sunanta da ya yi tun da farko.

Dakta Maryam ta kuma ce hakan bai karya mata gwiwa ba, domin kuwa a cewarta tana cike da ƙwarin gwiwar bauta wa ƙasarta.

”Ina son tabbatar wa magoya baya na cewa wannan ba shi ne ƙarshe ba, yanzu ma aka fara, don haka ku ci gaba da yi wa ƙaramu addu’a tare da goya wa shugaban ƙasarmu baya”.

A ranar Laraba ne shugaban ƙasar ya aike da sunayen mutum 19 ciki har da Dakta Maryam Shetti ga Majalisar Dattawan kasar domin tantance su a matsayin ministoci.

Sanya sunan Shetty cikin jerin sunayen ya janyo zazzafar muhawara musamman a shafukan sada zumunta a arewacin ƙasar, kasancewar sunan nata ya zo wa mutane da dama da mamaki.

To sai dai kuma a ranar Juma’a ana tsaka da tantance ministocin, sai shugaban kasar ya sake aika sunan mutum biyu zuwa majalisar, inda a ciki ya bayyana janye sunan Dakta Maryam Shetty, inda ya maye gurbinta da Dakta Mariya Mairiga Mahmud.

www.nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp