Ƙungiyar dattawan arewa ta magantu kan kisan matafiya ƴan yankin arewa da aka yi a garin Uromi da ke jihar Edo, inda ta ce yankin arewa ya daɗe yana haƙuri da cin kashin da ake yi masa, amma kuma an kusa ƙure su.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinta, Farfesa Abubakar Jika Jiddere ya fitar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sanarwar ta ce, “dattawan arewa sun damu matuƙa da kisan dabbanci da rashin tausayi da aka yi wasu mafarauta ƴan arewa da suke hanyarsu ta komawa gida arewa domin bikin sallah. Muna Allah wadai da wannan aika-aikar.
“Mun daɗe muna haƙuri da irin wannan cin kashin da ake mana a kudancin Najeriya. Dole a kawo ƙarshensa haka,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa dole a kama waɗanda suka aikata laifin, sannan a musu hukunci a bayyane.
“Sannan dole a biya diyyar waɗanda aka kashe kamar yadda yake a addinance, sannan dole gwamnatin Edo ta fito ta bayar da haƙuri.
Dattawan sun kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta Edo ta cika waɗannan buƙatun nan da kwana da 14, “idan kuma ba a ga wani mataki ba zuwa lokacin, dattawan arewa za su yi amfani da duk matakan da suka dace wajen bin haƙƙin ƴaƴanta da aka kashe.”