Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya yi alƙawarin hukunta mutanen da ke da hannu a kisan sojoji 14 ranar 14 ga watan Maris a jihar Delta.
Manyan jami’an soji huɗu da sojoji 12 aka kashe a lokacin da suke aikin wanzar da zaman lafiya bayan rikicin da ya faru a yankin Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli a jihar Delta.
“Hedikwatar tsaro da babban hafsan sojin ƙasa, sun samu amincewa ta hukunta duk wanda aka samu da hannu a mummunan aika-aikar da aka yi kan al’ummar Najeriya.” In ji Shugaba Tinubu.
Tinubu ya yi magana ne sa’oi bayan da kafafen yaɗa labarai suka ruwaito cewa wasu ɓata-gari sun cinna wuta kan gidaje da dama a yankin na Okuama yayin da mazauna wurin suka tsere saboda fargabar harin ramuwar gayya.