fidelitybank

Dole ne a ɗauki hukunci a kan waɗanda suka ƙona matafiya a Edo – Amnesty

Date:

Ƙungiyar Amnesty International mai fafutikar kare haƙƙin ɗan’adam ta ce, dole binciken da za a yi, ya zama sanadiyar hukunta waɗanda suke da hannu a kisa tare da ƙona matafiya ƴan arewa da aka yi a garin Uromi da ke jihar Edo.

Shugaban ƙungiyar a Najeriya, Isa Sanusi ne ya bayyana haka, inda, “dole hukumomin Najeriya su tabbatar an gudanar da bincike a bayyane, sannan kuma binciken ya zama silar adalci ga waɗanda aka kashe da iyalansu. Ya kamata a riƙa bayya yadda binciken ke gudana tun daga farko har zuwa lokacin yanke hukunci.”

Amnesty ta ce abin da ya faru Uromi na nuna yadda ake ƙara samun ƙungiyar ƴan sa-kai na garuruwan da suke kusa da manyan hanyoyi suke tare hanyoyin suna aikata ba daidai ba.

“Yadda aka daɗe ana irin waɗannan kashe-kashen na nuna akwai gazawar gwamnati wajen kare rayukan al’ummarta.”

Isa Sanusi ya ƙara da cewa Amnesty ta yi Allah wadai da kisan, sannan ya sake nanata kiransu ga gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakin da ya dace.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp