fidelitybank

Dole Najeriya ta cire rarar man fetur – Bankin Duniya

Date:

Babban Bankin Duniya, a jiya Laraba, ya yi gargadin cewa, Najeriya na fuskantar barazanar da za ta iya rusa ta.

World Bank ya yi gargadin cewa, idan Najeriyar ta gagara gyara tsarin tara harajinta da kuma mayar da hankali akan wasu bangarorin, domin bunƙasa kuɗaɗen shigarta, to ƙuɗaɗen shigarta za su ci gaba da raguwa.

Jaridar Punch ta ce, wani babban jami’i a Babban Bankin Duniyar, Mr Rajul Awasthi ne ya bayyana haka a wani taro akan muhimmanci yi wa tsarin haraji kwaskwarima domin cigaban kasa, wacce wata kungiyar sa ido kan tattalin arzikin Najeriya ta shirya.

Sannan jami’in ya haƙiƙance cewa, dole Najeriya ta cire rarar man fetur baki daya nan gaba.

World Bank ya bayyana cewa, duk da cewa farashin man fetur na ƙaruwa a kasuwannin duniya, Najeriya ba ta samu cin gajiyar wannan dama ba, saboda maƙudan kudaden da take kashewa akan rarar man fetur.

Wannan gargadi yana zuwa ne a lokacin da ƙudaden shigar Najeriya ke raguwa kuma tana cigaba da biyan tiriliyoyin nera akan rarar man fetur da matsalolin tattalin arziki.

news today in nigeria 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp