Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce a shirye gwamnatin tarayya take wajen binciko waɗanda suka jefa bom bisa kuskure a ƙauyen Tudun Biri na ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.
Kashim Shettima ya kuma tabbatar da cewa za a hukunta duk mutumin da aka samu da hannu a harin.
Ya kuma alƙawarta cewa gwamnatin tarayya za ta tallafa wa waɗanda suka jikkata a harin.
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci waɗanda suka jikkata a harin, wadanda ke kwance a asibitin koyarwa na Barau Dikko da ke birnin Kaduna.
Ya ce gwamnatin ƙasar a shirye take wajen kawar da ayyukan ta’addanci da fashin daji a yankin arewaci da sauran sassan ƙasar.