fidelitybank

Dole ce ta sa mu ke rabon abinci akai-akai – Zulum

Date:

Gwamnan jihr Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce dole ce ta sa gwamnatinsa ke yawan rabon tallafin abinci ga mabuƙatan jihar.

Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X ya ce gwamnatinsa na rabon tallafin ne domin magance wahalhalun da mutane suka shiga sakamakon rikicin Boko Haram, amma buƙatar gwamnatinsa shi ne kawo ƙarshen matsalar baki-ɗayanta.

Zulum ya ce yayin da gwamnatinsa ke raba tallafi ga mabuƙata da mutanen da rikicin Boko Haram da ya shafe fiye da shekara 10 ya shafa, a gefe guda kuma gwamnatin ta samu gagarumar nasara a wasu fannonin da suka shafi kiwon lafiya, da ilimi da tsaro da kuma ababen more rayuwa a jihar.

Gwamnan ya ce gwamnati na rabon tallafin ne domin rage raɗaɗi ga mutanen da suka rasa sana’o’insu sakamakon ayyukan ƙungiyar Boko Haram.

Mista Zulum ya kuma jaddada buƙatar samar da wata gidauniya da za a jima ana mora har na dogon zango, maimakon moro na lokaci guda, kamar rabon tallafi.

“Ba wai muna sa mutane su riƙa dogara da tallafin ba ne, kuna ganin ƙoƙarin da muke yi wajen farfaɗo da fannin noma, mutane su fahimci cewa dole ce take sa muke wannan abu. Mukan raba tallafi ne kawai ga mutanen da rikicin ya ɗaiɗaita, kuma sannu a hankali muna samun ci gaba”, in ji shi.

Gwamnan ya kuma duba yadda aka raba tallafin kayan abinci da wanda ba na abinci ba da kudin da suka kai naira miliyan 25 ga fiye da iyalai 25,000 a Gajiram, da ke ƙaramar hukumar Nganzai

nigeria peace corps

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp