Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira ga ƙasashen Majalisar Ɗinkin Duniya da cewa jazaman ne su tashi tsaye a kan abin da ya bayyana da “tsabagen takalar faɗa” daga Rasha.
A cewarsa, tabbatar da ‘yancin cin gashin kai na kowacce ƙasa da kare haƙƙin ɗan’adam jigo ne na tanade-tanaden da ke cikin daftarin Majalisar ƙasashen duniyan.
Joe Biden yana wannan jawabi ne a wani ɓangare na Babban Taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya na shekara-shekara a birnin New York.
A cikin shekara ta biyu a jere, ya ce, wannan taro ya yi duhu sakamakon inuwar wannan yaƙi, wanda Rasha ta haddasa ba tare da an takale ta ba.
“Rasha ta yi imanin cewa duniya za ta nuna gajiyawa, kuma duniya za ta bari Rasha ta zalunci Ukraine, ba da tare da sakayya ba.
Amma ina roƙonku wannan:
Idan muka bar waɗannan jiga-jigan aƙidoji na Daftarin Majalisar Ɗinki Duniya don lallaɓa mai takalar faɗa, shin wata ƙasa, wakiliyar wannan majalisa za ta samu ƙwarin gwiwar cewa tana da tabbataccen tsaro?
Idan muka bari aka yanki sashen ƙasar Ukraine, ko ‘yancin kowacce ƙasa, zai tabbata cikin tsaro?
Biden ya ce a’a.
“Hakan ce ta sa Amurka da abokan ƙawancenmu a faɗin duniya za su ci gaba da mara baya ga mutanen Ukraine masu jarumta a lokacin da suke kare ‘yancin cin gashin kai da mutuncin iyakokin ƙasarsu – da kuma ‘yancinsu.


