Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky, ya gaya wa taron shugabbanin ƙasashen G20 a Bali cewa dole a kawo ƙarshen yaƙin da Rasha ke yi a ƙasarsa.
Mista Zelensky wanda ya gabatar da jawabinsa ta bidiyo ya yi kira da a tsawaita yarjejeniyar fitar da hatsi daga ƙasarsa zuwa ƙasashen waje.
Ya ƙara da cewa ”Ina ganin yanzu ne ya kamata a kawo ƙarshen ɓarnar da Rasha ke yi mana a ƙasarmu da sunan yaƙi”
Shugaban Rasha Vladimir Putin wanda mamba ne a ƙungiyar ta G20 ya ƙi halartar taron, inda ya tura ministan harkokin wajen ƙasar Sergei Lavrov domin ya wakilce shi.