fidelitybank

Dole a kare hakkin Mata da ƙananan yara a Najeriya – UNICEF

Date:

Najeriya ta bi sahun ƙasashen duniya wajen gudanar da bikin gangamin yaƙi da zin zarafi mai nasaba da jinsi,da ƙungiyar Unicef ke jagoranta.

Gangamin na bana- mai taken ”zuba kuɗaɗe don yaƙi da cin zarafin mata da ‘yan mata”  ya jaddada ƙudurin gwamnati na magance duka nau’ikan cin zarafin mata da ƙananan yara.

Taron na bana wanda aka kwashe kwanaki 16 ana gudanarwa ya ƙarfafa wa mutane gwiwa wajen bayyana ƙudurinsu don magance matsalar cin zarafin mata da ‘yan mata ta hanyar musayar matakan da ake ɗauka don magance matsalar a faɗin duniya.

Haka kuma gangamin ya kuma buƙaci gwamnatoci da hukumomin duniya da su bayyana irin jarin da suke zuba wa don magance matsalar cin zarafin jinsi.

Cikin wata sanarwar ta Unifef ta fitar bayan taron, ta ce nau’ikan cin zarafin jinsi da ake aikatawa a Najeriya sun haɗar da fyaɗe da cin zarafin matan aure, da aikata lalata da auren wuri da kaciyar ‘ya’ya mata da sauran abubuwa, lamarin da ke tasiri ga matan ta fuskar tunani da zamantakewa da tattalin arzikinsu.

Sanarwar ta ce gwamnatin Najeriya ƙarƙashin ma’aikatar lafiya da ma’aikatar harkokin mata, sun haɗa hannu da hukumar Unicef da sauran masu ruwa da tsaki wajen wayar da kan al’umma wajen magance matsalolin da suka jiɓanci cin zarafin mata.

Wakiliyar Unicef a Najeriya, Cristian Munduate ta ce ”a hukumarmu mun fahimci cewa magance matsalar cin zarafin mata da ‘yan mata ba abu ne da ke buƙatar gaggawa ba, babbar buƙatarmu ita ce aiki da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki don magance matsalar tun daga tushe. A yanzu lokacin ɗaukar mataki ya yi, domin tabbatar da cewa mata da ‘yan mata sun rayu cikin aminci da karimci da girmamawa tare da ‘yanci”.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp