Rasha ta ce, ba za ta katse iskar gas da take sayarwa Turawan Yamma ba tukunna, game da sharaɗin da ta sanya musu cewa, sai dai su rinka biyan kuɗin cinikin da kuɗinta na Rouble maimakon Dala ko yuro.
A ranar Alhamis ne Shugaba Putin ya sanya wa wata doka hannu da ke tilasta wa masu sayen gas da man fetur ɗinta buɗe asusun ajiya da bankinta sannan kuma su biya kuɗin da rouble daga yau Juma’a.
Fadar Kremlin ta ce dokar ba za ta shafi odar da aka riga aka biya kuɗinta ba, amma zai shafi wadda aka yi bayan 1 ga watan Afrilu ko kuma zuwa tsakiyar watan.
Ƙasar na yunƙurin farfaɗo da darajar kuɗinta na rouble yayin da takukuman da ƙasashen Turai da Amurka suka ƙaƙaba mata suka dabaibaye tattalin arziƙinta.