Rahotonni na cewa akalla mutane biyu ne aka kashe a jiya Litinin tare da kona wata motar kirar Toyota Sienna a jihar Enugu da wasu ‘yan bindiga suka ce tana aiwatar da aiki a lokacin dokar zama a gida.
An ce ‘yan bindigar sun bude wuta a kan shahararren wurin shakatawa na Holy Ghost da misalin karfe 8:00 na safe, inda suka fatattaki ‘yan kasuwa da matafiya.
Direban motar Sienna da ta kone, wanda ya tsira da ransa, ya ce, yana tsaye a ’yan mitoci kadan daga motar yana jiran fasinjoji a lokacin da ’yan bindigar suka zo cikin wata karamar motar bas.
Ya ce, yana jin su ’yan fashi da makami ne suka gudu don ceto rayuwarsa, amma da ya waiwaya sai ya ga motar tana ci.
Rahotanni sun ce, ‘yan bindigar sun bude wuta a dajin, inda suka afkawa wasu fasinjoji. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Enugu, Daniel Ndukwe, bai amsa tambayoyin da aka yi masa kan lamarin ba a lokacin da manema labarai suka tuntubi shi.
Gwamnatin jihar IMO ta zargi ‘yan adawa da daukar nauyin masu aiwatar da wannan doka a jihar. Kwamishinan Yada Labarai da Dabaru, Cif Declan Emelumba, a wata sanarwa da ya fitar jiya, ya zargi ‘yan adawa da kitsa umarnin da kungiyar ‘yan awaren Biafra (IPOB) ta fara aiwatarwa, kafin kungiyar ta soke shi.
Sanarwar ta kuma baiwa ‘yan asalin jihar da mazauna yankin tabbacin samun tsira yayin da suke gudanar da harkokinsu.