fidelitybank

Dokar Zabe: Kanzon kurege ne kawai batun sa hannun ‘yan majallisu – Gbajabiamila

Date:

Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yi watsi da rahotannin kafafen yada labarai na cewa ‘yan majalisar sun fara tattara sa hannu, domin kalubalantar kin amincewa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari na kin amincewa da gyara dokar zabe.

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne ga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da suka yi da Buhari a fadar da ke Abuja.

Shugaban majalisar ya na tare da shugaban kasa da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa, Gbajabiamila na cewa “Mu na hutu a yanzu. Tarin sa hannu ba abu ne da a ke yi ba lokacin da mu ke hutu, lokacin da kowa ya watse. Abin da na fada a fili, na bayyana karara a zaman mu na karshe, cewa za mu dubi matakin kin amincewar shugaban kasa da dalilansa. Kuma idan mu ka dawo, ba abin da za mu yi a gwiwa ba ne.

“Lokacin da muka dawo daga hutun mu, har yanzu akwai isasshen lokaci, za mu yanke shawara ɗaya ko wata hanya. Wace hanya za a bi, zaɓuɓɓuka suna nan. Za mu yi abin da ya dace ga al’ummar Najeriya. Kuma na bayyana karara cewa ba za mu watsar da ruwan wankan da ya ke dauke da jariri ba,” inji Gbajabiamila

“Yan Najeriya su na so kuma ‘yan Najeriya za su samu. Wataƙila mun dakata kaɗan. Amma idan mu ka dawo, dama, akalla har zuwa majalisa, kuma na tabbata majalisar dattawa ita ma, ita ce abu na farko a ajandar mu, a makon da mu ke dawowa daga hutu.

Shugaban Majalisar Dattawan, wanda ya kuma yi magana da ‘yan jarida, ya ce kudirin kasafin kudi na shekarar 2022 na N17.13tn da a ka amince da shi kwanan nan za a mika shi ga shugaban kasa nan da mako mai zuwa, domin sanya hannu.

nigeria 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp