fidelitybank

Dokar Haraji ba za ta tabbata ba dole sai da masu ilimin abun – Barau

Date:

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibril, ya ce Majalisar Dattawa ta yi wa ƙudirin haraji karatu na biyu ne domin a samu damar miƙa shi ga kwamitin kuɗi domin bibiyarsa da faɗaɗa nazari a kansa.

Cikin wata hira da BBC Sanatan mai wakiltar Kano ta Arewa ya ce, majalisar ta bayar da shawarar miƙa wa kwamitin kuɗi ya duba tare da shirya jin ra’ayin jama’a, kuma hakan ba zai yiwu ba har sai an yi wa ƙudirin karatu na biyu.

”E an ji an yi jawabai, kuma mu a nan majalisa za mu iya tambayarsu, amma ‘yan Najeriya ba za su samu damar yin tambaya game da ƙudirin ba har sai an kira jin ra’ayin jama’a”.

Sanata Barau ya ce dokar haraji ba za ta tabbata ba dole sai da masu ilimin haraji, ”kan haka ne yanzu aka tura domin su je su duba, su feɗe komai sannan su yi mana bayanin abin da ya ƙunsa”.

Ƙudirin harajin – da majalisar dattawan ta yi wa karatu na biyu a makon nan – ya haifar da ce-ce-ku-ce musamman tsakanin wasu ‘yan arewacin ƙasar, da ke zargin cewar ƙudirin zai cutar da yankin.

To amma mataimakin shugaban majalisar ya ce karatu na biyu ba shi ke nuna cewa majalisar ta amince da ƙudurin ba, ”ai a nan ne ma aikin yake farawa”.

legitnews.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp