Tiktok ya daina aiki a Amurka, yayin da dokar da hukumomin ƙasar suka sa ta dakatar da manhajar daga ranar 19 ga watan Janairu, 2025 ta fara aiki.
Daman kuma tun ‘yan sa’o’i gabanin sabuwar dokar ta fara aiki manhajar ta daina aiki a wayoyin wasu Amurkawa da dama.
Sakon da ke bayyana a manhajar ga masu amfani da ita a Amurka shi ne dokar hana amfani da manhajar ta fara aiki – hakan na nufin ba za ku iya amfani da TikTok ba yanzu
Amurka ta haramta amfani da manhajar ne saboda damuwar da take nunawa cewa tana da alaka da gwamnatin China, kuma ta ba ta wa’adin zuwa yau 19 ga watan Janairu, masu manhajar su sayar wa wani kamfanin Amurka.
Haramcin ga Tiktok na zuwa ne jim kadan bayan da ƴan majalisar ƙasar suka nuna damuwa kan tsaron ƙasar.
Wakiliyar BBC ta ce zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ya ce akwai yiwuwar zai tsawaita lokacin da aka dibarwa Tiktok din zuwa kwana casa’in da zarar ya shiga ofis a gobe Litinin
A ƙarƙashin dokar ta yanzu, a lokacin haramcin kamfanin mallakar wasu yan China za su ci gaba da tattaunawa da wani kamfani na Amurka domin sayar da manhajar, matakin da ‘yan Chinan suka ƙi amincewa da shi.