fidelitybank

Direbobin Tifa hudu sun shaki iskar ‘yanci a Kwara

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, a ranar Alhamis, ta tabbatar da sakin wasu direbobi hudu da aka yi garkuwa da su ranar Laraba a wajen garin Ilorin, babban birnin jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Mista Okasanmi Ajayi ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis cewa, mutanen hudu da aka yi garkuwa da su sun samu ‘yanci daga wurin masu garkuwa da mutane kuma yanzu suna tare da iyalansu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa, ana ci gaba da kokarin kamo masu shirya wannan aika aika.

Ko da yake wata majiyar iyalan daya daga cikin direbobin da aka sako ta bayyana cewa an biya kudin fansa ne domin ‘yancinsu, amma rundunar ‘yan sandan ta yi shiru kan batun saboda rashin hakura da biyan kudin fansa daga iyalan wadanda aka sace.

Okasanmi, ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa ‘yan sanda bayanan da zai sa su samu nasarar aikin da suka yi.

Rahotanni sun ce, an yi wa direban tipper din kwanton bauna ne wasu mutane sanye da Uniform na sojoji suka tafi da su a wani wurin da suka je diban yashi.

Mutanen hudu da abin ya rutsa da su, an ce mambobin kungiyar masu sayar da kwalaye da yashi ne reshen garejin Oyun na Ilorin.

Masu garkuwa da mutanen, wadanda daga baya suka tuntubi iyalansu, sun bukaci kowanne iyalan da abin ya shafa a biya su Naira miliyan 5.

An ga direbobin Tifar a tsohuwar hanyar Jebba-Ilorin, dai dai da kusa da harabar kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kwara a ranar Laraba, kafin faruwar lamarin.

kano news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...
X whatsapp