Direbobin manyan motoci wadanda ke mara wa shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro baya, sun toshe tituna a fadin kasar, bayan da shugaban kasar ya sha kaye a zaben zagaye na biyu da aka gudanar a karshen mako.
Rahotonni sun ce, an rufe tituna a duka jihohin kasar in banda guda biyu, lamarin da ya haddasa cunkoso tare da shafar jigilar kayan abinci a fadin kasar.
Sakamakon zaben ya nuna cewa tsohon shugaban kasar Luiz Inácio Lula da Silva ne ya yi nasara da dan karamin rinjaye kan abokin karawarsa, kuma shugaban kasar Jair Bolsonaro.
Mista Bolsonaro dai bai kalubalanci sakamakon zaben ba, duk kuwa da cewa bai bayyana amincewa da shan kayen ba.
Akwai fargabar cewa shugaban kasar zai haifar da rudani a kasar cikin watanni biyu da suka rage kafin ya mika mulki ga sabon shugaban kasar.
Za dai a rantsar da zababben shugaban kasar ranar daya ga watan Janairun 2023.