fidelitybank

Direbobi hudu sun shaki iskar ‘yanci a Kwara

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, a ranar Alhamis, ta tabbatar da sakin wasu direbobi hudu da aka yi garkuwa da su ranar Laraba a wajen garin Ilorin, babban birnin jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Mista Okasanmi Ajayi ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis cewa, mutanen hudu da aka yi garkuwa da su sun samu ‘yanci daga wurin masu garkuwa da mutane kuma yanzu suna tare da iyalansu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya bayyana cewa, ana ci gaba da kokarin kamo masu shirya wannan aika aika.

Ko da yake wata majiyar iyalan daya daga cikin direbobin da aka sako ta bayyana cewa an biya kudin fansa ne domin ‘yancinsu, amma rundunar ‘yan sandan ta yi shiru kan batun saboda rashin hakura da biyan kudin fansa daga iyalan wadanda aka sace.

Okasanmi, ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa ‘yan sanda bayanan da zai sa su samu nasarar aikin da suka yi.

Rahotanni sun ce, an yi wa direban tipper din kwanton bauna ne wasu mutane sanye da Uniform na sojoji suka tafi da su a wani wurin da suka je diban yashi.

Mutanen hudu da abin ya rutsa da su, an ce mambobin kungiyar masu sayar da kwalaye da yashi ne reshen garejin Oyun na Ilorin.

Masu garkuwa da mutanen, wadanda daga baya suka tuntubi iyalansu, sun bukaci kowanne iyalan da abin ya shafa a biya su N5m.

An ga direbobin tipper a tsohuwar hanyar Jebba-Ilorin, dai dai da kusa da harabar kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kwara a ranar Laraba, kafin faruwar lamarin.

@nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kai hari a ƙauyuka 15 na Zamfara a mako ɗaya – Rahoto

Wani rahoto da tashar Channels ta ruwaito daga cibiyar Zamfara Circle...

Jihohin Arewa huɗu ne suke biyan mafi ƙarancin fansho na N32,000 – NUP

Ƙungiyar ƴan fansho na arewacin Najeriya, NUP ta ce...

A karon farko an gurfanar da Mutanen da ake zargi da kai hari Cocin Owo

Mutum biyar da ake zargi da shirya harin bam...

Peter Obi na nan a cikin jam’iyyar har yanzu – LP

Shugaban ƙungiyar Obidient Movement, Dr. Tanko Yunusa ya ce...

Yadda Mahara sun kashe mutum biyu, sun ƙona gidaje a Filato

Wasu da ake zargin mahara sun afka wa karamar...

An YI zanga-zanga a Isra’ila kan shirin Netanyahu na mamaye Gaza

Dubban mutane sun fito kan tituna a faɗin Isra'ila,...

Birtaniya za ta fara tisa ƙeyar bakin da suka aikata laifi zuwa kasarsu

Birtaniya ta fitar da sabon tsarin tisa keyar duk...

NDLEA ta kama Fasto kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya,...

Gwamnoni sun mika sakon ta’azziya ga iyalan Audu Ogbeh

Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu...

Duk wahala sai dai mu mutu a Gaza – Fatma

Wata mai mai ƴaƴa tara ta ce, duk runtsi...

Gwamnan Kano ya kori mataimansa na musamman kan belin Danwawu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da...

Tsohon Minista a mulkin Buhari ya mutu

Allah ya yi wa tsohon ministan noma da raya...
X whatsapp