Rundunar ‘yan sandan jihar Edo, ta ce, direban shugaban kungiyar dillalan man fetur ta kasa reshen jihar, Alhaji Abdul-Hamid Egele, ya rasu.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, SP Kontongs Bello, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN rasuwar a ranar Talata da daddare.
Marigayin, wanda ba a iya tantance ko wanene shi, ya na tuka motar Egele ne, a lokacin da ‘yan bindiga suka kai musu hari inda suka yi awon gaba da shi.
An yi garkuwa da Egele ne a gidansa na Jattu da yammacin ranar Litinin, yayin da mahara suka tare ayarin motocinsa, inda suka kashe direbansa nan take.
‘Yan bindigar sun kuma harbe direban na biyu da jami’in tsaron da ke tare da shi tare da raunata shi.