Jam’iyyar PDP reshen jihar Kogi, ta bayyana Sanata Dino Melaye a matsayin wani nauyi da ya rataya a wuyan jam’iyyar, cewa ba shi da amfani kuma ƙajagane.
Dattawan jam’iyyar PDP a jihar karkashin jagorancin Ibrahim Dansofo, sun bukaci kwamitin zartarwa na karamar hukumar Ijumu da su fara shirin dakatar da Melaye cikin gaggawa.
Hakan a cewarsu, zai jaddada bukatar dawo da martabar jam’iyyar tare da mai da hankali kan ingantaccen shugabanci.
A ranar Asabar, Melaye ya ce mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iliya Damagum, Samuel Anyanwu da Umar Bature sun lalata tsohuwar jam’iyya mai mulki.
Melaye ya yi ikirarin cewa, sarakunan uku sun lalata jam’iyyar PDP ba tare da tabuka komai ba.
Da suke yin Allah wadai da kalaman nasa, dattawan jam’iyyar sun ce, burin siyasar Melaye ya durkushe har ta kai ga ya kasa samun mukamin kansila.
Dattawan da Dansofo ke jagoranta sun bayyana Melaye a matsayin abin da ya rataya a wuyansu, inda suka nuna cewa ci gaba da cudanya da jam’iyyar ya yi ne kawai don tattaunawa da jam’iyya mai mulki maimakon bayar da gudunmawa mai kyau ga PDP.
“Sanata Melaye ya zama nauyi ga jam’iyyar.
“Zarge-zargen da ya ke yi wa shugabanni na yanzu munafunci ne, domin shi da kansa an ba shi tikitin takarar gwamna duk da sanin jam’iyyar na rashin iya cin zabe ko da zaben fidda gwani,” in ji Dansofo.
Jam’iyyar PDP ta Kogi ta dora laifin gwagwarmayar da jam’iyyar ke yi a halin yanzu a kafadar Melaye, inda ta ce zaben nasa wani babban kuskure ne da ya kai su ga halin da suke ciki a halin yanzu.
Daga karshe sun yi kira ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Gwamna Ifeanyi Okowa da su sake duba goyon bayansu ga Melaye, inda suka bukaci su nisanta kansu da wani da suka bayyana a matsayin “kangi” da kuma babban nauyi ga jam’iyyar.
Sun yi kira ga al’ummar Najeriya da su yi watsi da kalaman Melaye, tare da lakafta su a matsayin kalaman da ba a taba gani ba na mutumin da dacewar siyasarsa ta dade da dusashewa.
“Jam’iyyar PDP ta Kogi ta kuduri aniyar ci gaba, ta maido da karfinta da kuma dawo da martabarta a matsayin babbar jam’iyyar siyasa a jihar, masu ruwa da tsakin sun bukaci Dino Melaye da ya yi lissafin biliyoyin da ya tara da sunan zaben gwamna,” in ji su.