Tsohon ɗan jamalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya koma jam’iyyar haɗakar ADC bayan ficewarsa daga PDP.
Cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, an ga yadda Dino Melaye ya karɓi katin jam’iyyar ADC daga hannun jagororin jam’iyyar na ƙaramar hukumarsa.
Tun da farko a yau ne Dino Melaye ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP bayan ya rubuta wa jagororin jam’iyyar na mazaɓarsa ta Aiyetoro Gbede wasiƙar ficewarsa daga jam’iyyar.
A cikin wasiƙar Melaye ya bayyana dalilan kasawar jam’iyyar wajen magance matsalolin da ke damunta.
”Matakin ya zama wajibi saboda gazawar jam’iyyar wajen ceto yan Najeriya daga cikin kuncin da ƙasarmu ke ciki”, kamar yadda wasiƙar ta bayyana.
Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kogin na jam’iyyar PDP ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari kan halin da jam’iyyar ke ciki.