Wasu mata ‘yan asalin Najeriya da suka tafi neman aiki a kasashen Larabawa na yankin Gabas ta Tsakiya, sun makale a Dubai.
Da dama daga cikin matan dai na cikin mawuyacin hali bayan da suka ce ejandinsu ya zambace su tare da yaudarar cewa zai samar musu aiki amma hakan bai yiwu ba.
Wasu daga cikin wadannan mata da BBC ta tattauna da su sun ce, an yaudare su ne a kan cewa za a sama musu aiki shi ya sa suka bar kasarsu ta asali suka tafi can.
Wata daga cikinsu da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa BBC cewa, yanzu haka tana Dubai inda ta je ta sanadiyyar ejadinta don a sama mata aiki.