Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce, dimokuradiyya ta kasa aiwatar wa matasa abun da suke so tsawon shekaru 23 da komawar ta kasar.
Gbajabiamila ya bayyana haka ne a ranar Litinin, a yayin bikin bude wani shiri na horas da matasan Najeriya na Legislative Mentorship Initiative.
Ya bayyana cewa akwai bukatar ‘yan Najeriya su zabi shugaban da zai iya tafiyar da sauye-sauye, ya kara da cewa ba zai yiwu ba a sa ran matasa su ci gaba da rike amanar dimokradiyya.
“Ba daidai ba ne a yi tsammanin matasan kasarmu za su jajirce wajen dorewar dimokuradiyyar da ba ta cimma burinsu ba,” in ji shi.
Kakakin majalisar Gbajabiamila ya jaddada cewa yawancin matasa a kasar, ba su shaida gwamnatin mulkin soja ba, don haka, ba za a yi tsammanin za su jajirce wajen tabbatar da dimokuradiyya ba tare da cin gajiyar ta ba.
Ya ce, “Najeriya na matukar bukatar shuwagabanni masu kwazo da halayya don tafiyar da canji. Sakamakon canje-canjen da ke faruwa a duniyarmu a yau zai dogara ne akan yadda muke amsawa, yanke shawara da muka yanke, da kuma ra’ayoyin da muka zaɓa don saka hannun jari a ciki. ”
Domin magance matsalar, Gbajabiamila ya ce “dole ne mu yi gaggawar daukar matakin shigar da matasa cikin harkokin siyasa da mulki. Muna yin hakan ne ta hanyar samar da hanyoyin ci gaban jagoranci”.