Shugaban kasa Muhammadu Buhar,i ya nada Alhaji Salihu Abdulhamid Dembos, a matsayin Darakta-Janar na hukumar gidan talabijin ta kasa, NTA.
Ministan yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya ba da sanarwar a Abuja yau Laraba.
Ya ce mukamin na wa’adin shekara uku ne a karon farko.
Kafin ba shi mukamin, Mr Dembos ya rike mukamin babban daraktan sashen tallace-tallace na NTA.
Mr Dembo ya shafe sama da shekara 20 yana aikin jarida, kuma ya yi aiki a matsayin Janar Manaja a Lokoja da Kano, da kuma daraktan NTA reshen Kaduna.


