fidelitybank

Deji ya yi tir da dabi’un Melaye na tanakawa a kan lafiyar Tinubu

Date:

Shahararren dan gwagwarmayar zamantakewa da siyasa, Deji Adeyanju, ya yi Allah wadai da matakin da kakakin jam’iyyar PDP, kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, PCC, Dino Melaye, ya dauka na yin ba’a ga yanayin lafiyar dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

Melaye dai ya yi barkwanci ne game da yanayin lafiyar Tinubu ta hanyar rawan ba’a a yayin wani gangamin yakin neman zabe a jihar Delta a ranar Talata.

Da yake mayar da martani game da ci gaban, Adeyanju, a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar Laraba, ya bayyana matakin Melaye a matsayin “mara kyau kuma ba za a yarda da shi ba”.

Ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, “Yin ba’a ga wani saboda yanayin lafiyarsa ba shi da kyau.

“Kuna iya neman a ba da lissafi da cikakken bayyanawa daga wanda ke son zama shugaban kasa har ma da kushe su kan wannan amma ba’a a fili ba abin yarda ba ne.”

Wannan dai ba shine karo na farko da Melaye ke yiwa Tinubu ba’a ba.

A kwanakin baya ne dan siyasar haifaffen Kogi ya kalubalanci Tinubu da ya karanta Fatiha da surori uku domin ya nuna cewa shi Musulmi ne na gaskiya.

ng news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp