Mai kungiyar West Ham David Sullivan, ya amince Declan Rice ya buga wasansa na karshe a kungiyar bayan lashe gasar cin kofin Europa.
Ana alakanta Rice da Arsenal, Manchester United, da Bayern Munich.
Yanzu Sullivan ya ce dan wasan na Ingila zai yi tafiya, domin ya kuduri aniyar barin kulob din na Landan.
“Ina ganin dole ne ya zama [wasansa na karshe]. Mun yi masa alkawari zai iya tafiya. Ya saita ransa zai tafi.
“Ba za ku iya neman mutumin da ya ƙara mana himma a wannan kakar ba. A lokacin da ya dace, dole ne ya ci gaba, kuma dole ne mu sami wanda zai maye gurbinsa ko wasu da yawa,” Sullivan ya shaida wa talkSPORT.
Sullivan ya kuma yi ikirarin cewa an ba Rice fam 200,000 a mako don ya zauna tare da Hammers watanni 18 da suka wuce, amma ya ki.
Ya kara da cewa “An ba shi fam miliyan 10 don ya ci gaba da zama a West Ham a wancan lokacin.”