Mai tsaron ragar Manchester United, David De Gea, ya lashe kyautar gwarzon dan wasan EA SPORTS na watan Janairu 2022.
Dan kasar Sipaniya ya zama mai tsaron gida na farko da ya lashe kyautar kowane wata tun watan Fabrairun 2016, lokacin da Fraser Forster na Southampton ya lashe kyautar.
De Gea ya yi nasarar ceto ƙwallaye sau 22 a wasanni hudu da Manchester United ta yi a watan Janairu, inda ya aka zura masa ƙwallo biyar kacal a wasan da Wolverhampton Wanderers ta doke su da ci 1-0, bakwai a wasan da suka tashi 2-2 da Aston Villa, sannan kuma ya kara takwas wanda hakan ya sa aka ci 3-1 Brentford.