Dan wasan tsakiya na Manchester City, Kevin De Bruyne, a daren Laraba, ya daidaita tarihin taimakawa da tsohon dan wasan Manchester United David Beckham.
De Bruyne ya samu wannan nasarar ne bayan ya taimaka wa abokin wasansa Erling Haaland a wasan da Manchester City ta yi a gasar zakarun Turai da suka tashi 1-1 da Bayern Munich a daren jiya.
Taimakon shi ne na 259 na De Bruyne na taimaka wa aiki, wanda ya yi daidai da tarihin Beckham kuma ya yi a cikin mintuna 15,000 fiye da tsohon kyaftin din Ingila.
Ba za a dade ba De Bruyne zai haye tarihin Beckham, kuma na gaba a idon sa akwai dan wasan Al-Nassr Cristiano Ronaldo wanda ya taimaka 268 da kuma Angel di Maria na Juventus, ya taimaka 277.
Sakamakon wasan na nufin ‘yan wasan Pep Guardiola sun samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai da ci 4-1 jimilla, bayan da suka doke Bayern Munich da ci 3-0 a wasan farko a makon jiya a filin wasa na Etihad.
Yanzu dai Man City za ta kara da Real Madrid a wasan kusa da na karshe a gasar zakarun Turai a watan Mayu.


