Gunde Mark, ɗan tsohon shugaban majalisar dattijai, Sanator David Mark, ya mutu.
Wani daga cikin iyali ya ce, Sunde ya mutu a Juma’ar nab a Landan, Ingila.
Rahotanni na cewa, ya sha fama da cutar kansa kuma ya mutu yana da shekara 51.
Ya sami digiri na B.SC daga Kwalejin Singar, London. Daga baya ya ci gaba da yin nazarin kimiyyar halittu a makarantar Harvard, da Cambridge, Massachusetts.
Ya bar mace da yaro.