Fitaccen mawakin Najeriya, Davido, ya nuna godiya ga hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, saboda ba shi damar kasancewa cikin tawagar da ta yi aiki a fagen waƙa na wannan shekarar a gasar cin kofin duniya.
Waƙar mai taken, Hayya Hayya, ma’ana Better Together, Davido ya rubuta a shafin sa na Twitter cewa, “Na yi farin ciki da fitowa a cikin mawaƙan gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022.
A cewarsa, haɗin gwiwar da Trinidad Cardona da Aisha nasara ce ga Afirka, bisa yadda suka raira waƙar.