Wani dattijo mai shekaru 60, Malam Danjuma, wanda aka fi sani da “Black”, da dansa, Ibrahim mai shekaru 35, da kuma Aminu Gaye, mai shekaru 35, sun mutu a cikin wani rami a bayan gida a lokacin da suke kokarin karbo wayar salula.
Saminu Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi.
Ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa daga tashar kashe gobara ta Tsanyawa da misalin karfe 11:00 na safe cewa wasu mutane hudu sun makale a cikin wani bandaki.
A cewarsa, Danjuma yana kokarin dauko wayar salula da ta fada cikin bandakin ramin, sai ya makale. Bayan haka, dansa ya shiga bandaki ramin don ya ceci mahaifinsa shi ma ya kama shi.
“Gaye da Alasan suma sun shiga ne domin ceto mutanen biyu kuma sun makale,” in ji shi.
Abdullahi ya ce an kubutar da mutum uku na farko da suka mutu a sume, yayin da na hudun kuma aka ceto da ransa.
Ya ce an mika dukkan wadanda abin ya shafa ga Sufeto Iro Lado, a sashin ‘yan sanda na Tsanyawa.
Abdullahi, ya ci gaba da cewa, rundunar ‘yan sandan ta kai wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin musamman na Bichi domin kula da lafiyarsu, inda likitocin da ke bakin aiki suka tabbatar da mutuwar mutane uku da kuma daya na raye.