Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya bayyana yadda wasu dattawan jihar suka yi masa katsalandan, saboda ba su yi zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar ba.
Wike ya bayyana cewa, wasu daga cikinsu da suka nuna sha’awarsu na daga tutar jam’iyyar amma suka kasa, sun je Abuja ne domin su tabbatar da cewa bai fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin cika shekaru 74 da haihuwa da aka shirya domin karrama tsohon gwamnan Ribas, Dakta Peter Odili, a gidansa da ke Unguwar Tsohuwar Gwamnati a Fatakwal, ranar Litinin.