An gudanar da jana’izar fitaccen daraktan Kannywood, Aminu S. Bono a safiyar yau a ƙwaryar birnin Kano.
Manyan ‘yan masana’antar ta Kannywood da dama ne suka halarci jana’izar a unguwar Ɗandago da ke birnin Kano.
Daraktan na Kannywood ya rasu ne a jiya Litinin, bayan ya yanke jiki ya faɗi jim kaɗan bayan ya koma gida daga wurin aiki.