Darajar naira ta faɗi ƙasa warwas zuwa matsayi mafi ƙasƙanci da aka gani a shekarun baya-bayan nan, inda aka canzar da dala ɗaya a kan naira 1,043.09 a cibiyar hada-hada da farashin hukuma ranar Alhamis.
Jaridar Daily Trust ta ce sabon farashin ya zarce na 872.59 a kan dala ɗaya da aka canzar da naira ranar Laraba a cibiyar hada-hadar kuɗaɗen waje ta Najeriya (NAFEM).
Alƙaluma daga cibiyar hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje ta FMDQ sun nuna cewa an samu ƙarin shigar dalar Amurka da kashi 38.81 zuwa dala miliyan 127.93 a ranar Laraba daga dala miliyan 92.16 a ranar Juma’a ta makon jiya.
Masu saye da sayarwa da ke hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje a cibiyar ta NAFEM ne suke kai dalar.
Masharhanta sun fitar da ƙididdigar cewa Naira na cikin kuɗaɗen duniya waɗanda darajarsu ke ta yi matuƙar faɗuwa a shekara ta 2023.