Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya zama shugaban kungiyar gwamnonin Kudu.
Gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya zama mataimakin shugaba.
Hakan ya biyo bayan wani taro da kungiyar gwamnonin Kudu suka yi a Abeokuta, jihar Ogun, a ranar Litinin.
Taron wanda ya dauki kimanin sa’o’i biyar, ya samu halartar gwamnoni 13 da mataimakan gwamnoni uku daga jihohin Kudu.
Gwamnonin sun hada da Dapo Abiodun, Ogun, Godwin Obaseki, Edo, Seyi Makinde, Oyo, Alex Otti, Abia, Babajide Sanwo-Olu, Legas, Ademola Adeleke, Osun, Francis Nwifuru, Ebonyi, Peter Mbah, Enugu, Douye Diri, Bayelsa. da Umo Eno, Jihar Akwa Ibom.
Sauran sun hada da Biodun Oyebanji, Ekiti, Bassey Otu, Cross River, Charles Soludo, Anambra, mataimakin gwamnan jihar Imo, Chinyere Ekomaru, mataimakin gwamnan jihar Delta, Monday Onyeme, da mataimakin gwamnan jihar Ondo, Olayide Adelami.