Hamshakin ɗan kasuwar nan, Aminu Alhassan Dantata ya bayar da tallafin naira biliyan 1.5 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a wasu sassan Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Attajirin ɗan jihar Kano ya bayar da tallafin ne a lokacin da ya jagoranci wata tawaga daga Kano zuwa gidan gwamnatin Borno Maiduguri ranar Talata.
Ya mika ta’aziyyarsa ga Gwamna Babagana Zulum, da gwamnati da kuma al’ummar jihar baki ɗaya, musamman mutanen da suka rasa ƴan’uwansu a ambaliyar ruwa.
Dantata mai shekaru 96, ya koka kan tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya, inda ya bukaci masu fada-a-ji da shugabannin siyasa su ji tsoron Allah a yadda suke gudanar al’amuransu.
Da yake mayar da martani, Gwamna Zulum ya nuna matukar godiya ga dattijon bisa ziyarar da ya kai masa, inda ya yi nuni da cewa hakan wata alama ce ta yadda jama’a ke tallafawa juna a lokutan tahsin hankali.
Shi ma attajiri Aliko Dangote ya bayar da tallafin naira biliyan ɗaya domin agaza wa waɗanda ambaliyar ta ɗaiɗaita.