Da sanyin safiyar Juma’a ne kungiyar ‘yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Katsina ta zabi tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Kananan Hukumomin Najeriya, Dakta Dikko Radda, a matsayin dan takararta a zaben gwamna na 2023.
Radda ya doke sauran ‘yan takara takwas inda ya zama zakara.
Jami’in zaben fidda gwani, Barista Kaka Lawa ne ya sanar da sakamakon zaben a wurin gudanar da atisayen, filin wasa na Muhammed Dikko, Katsina.
Lawan ya ce Radda ya samu kuri’u 506 inda ya doke sauran ‘yan takara.
Ragowar ’yan takarar da kuma zabukan da suka samu sun hada da: tsohon sakataren gwamnatin jihar, Muhammed Inuwa, 442; Tsohon Manajan Daraktan Kamfanin Tsaro da Buga na Najeriya, Alhaji Abbas Masanawa, 436; Musa Dangiwa,220; Tsohon kwamishinan tsare-tsare na kasafin kudi na jihar, Hon. Faruq Jobe, kuri’u 71; da mataimakin gwamnan jihar, Manir Yakubu, da kuri’u 65.
Sauran kuma makinsu sun hada da Abubakar Yaradua, kuri’u 32; Alhaji Umar Baure, kuri’u 8; da A. Dauda, kuri’u 7