Wani ɗan sanda a kasar Kenya ya harbe matarsa da wasu mutum biyar har lahira, sannan ya kashe kansa.
Lamarin ya faru ne a Nairobi, babban birnin ƙasar. Wasu mazauna unguwar Kebete, sun ce sun jiyo ƙarar harbi daga gidan Benson Imbasi rana Talata da sassafe. Inji BBC.
Bayan nan ya fito daga gidan ya kuma harbi mutum bakwai, biyar daga ciki suka mutu, aka kai biyu asibiti da raunuka.
Ma’aikacin ya kuma harbi kansa a wuya kuma ya mutu nan take, kamar yadda rahoton ‘yan sanda ya bayyana.