Matatar mai ta Dangote da ke Najeriya za ta gina wani rumbun ajiyar man fetur a ƙasar Namibiya domin adana ganga miliyan 1.6 na man fetur da dizel domin sayarwa a ƙasashen kudancin Afirka.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wasu majiyoyi na cewa za a yi amfani da rumbun wajen yin hada-hadar fetur a ƙasashen Botswana, da Namibiya, da Zambiya, da kuma Zimbabwe.
Haka kuma, Dangote na duab yiwuwar fara kai man fetur zuwa ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
Wani jami’i a hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Namibiya ya tabbatar wa Reuters shirin, yana mai cewa za a gina ma’adanar ne a yankin Walvis Bay da ke ƙasar.
A watan da ya gabata ne wata majiya ta bayyana cewa matatar Dangote ta fara sayar da mai zuwa nahiyar Asiya, karon farko da matatar ta yi hakan a wajen nahiyar yammacin Afirka.